Friday, 15 February 2019

Dan majalisa ya saci burodi a shago

Wani dan majalisa ya sauka daga amukaminsa bayan da ta bayyana cewa ya saci burodi samfurin sandwich a wani shago da ke birnin Lublyana bayan ya ce ma'aikatan shagon sun ki kula shi.


Dan majalisa Darij Krajcic kasar Slovenia ne.

Ya fada wa manema labarai cewa ya fusata ne bayan da ma'aikatan shagon suka "mai da ni tamkar iska", shi yasa ya ce ya gwada tsarin tsaron shagon, inda ya fita da burodin ba tare da ya biya kudinsa ba.Babu wanda ya lura ya saci burodin bayan ya fice da shi, amma dan majalisar wanda dan jam'iyya mai mulkin kasar ce ta Marjan Sarec List (LMS) ya ce ya koma daga baya ya biya kudin burodin.

Mista Krajcic ya nemi a yi masa afuwa kuma ya ce ya yi nadamar abin da ya aikata.

Da kansa ya bayyana abin da ya faru a majalisa inda ya fada wa wasu abokan aikinsa komai a lokacin wani taro na wani kwamiti da yake cikinsa.


"Na tsaya a gaban kantar shagon na tsawon akalla minti uku," inji dan majalisar mai shekara 54 a wata hira da yayi da tashar talabijin ta Channel POP.

Ya ce ma'aikatan shagon uku suna tsaye a kusa amma basu damu da shi ba, shi yasa kuma suna tadi a tsakaninsu, sai ya gwada ficewa ba tare da ya biya kudin burodin ba.

Kafin zuwansa majalisa, Mista Krajcic ya taba zama malamin makaranta.

"Babu wanda ya biyo ni, babu wanda yayi ihu", inji shi, inda ya kuma ce da alama mutane sun faye mayar da hankali kan amfani da na'urar CCTV a maimakon sa ido.

Da farko abokan aikinsa 'yan majalisa sun dauki abin da wasa, amma ranar Alhamis sai shugaban wani tsagi na jam'iyyar LMS Brane Golubovic ya soki abin da Mista Krajcic yayi.

An dai zabi Mista Krajcic ne a watan Satumbar bara, a lokacin da jam'iyyar Firai Minista Marjan Sarec ta LMS ta zama babbar kawa a hadakar jam'iyyu masu mulkin kasar Slovenia.
BBCHausa.

No comments:

Post a Comment