Monday, 11 February 2019

DAN NIJERIYA YA KAFA TARIHI A DUNIYA:Ya Kirkiri Na'urar Da Za Ta SA Mota Ta Tuka Kanta

Professor Dr. Idris Ahmed Phd Cryptology Maigidana kuma Masoyina dan Nigeria haifaffen garin Mubi jihar Adamawa mazaunin birnin Coventry a Kasar Burtaniya ya kafa tarihi, domin ya samu nasarar gina fasahar tsaro na na'ura mai kwakwalwa akan mota wacce za ta iya tuka kanta.


Sanannen kamfanin kera mota na duniya dake Kasar Burtaniya wato "Jaguar Land Rover" sun bawa Dr. Idris Ahmed kwangila tun kusan shekara daya da ya gabata a karkashin Kamfaninsa mai suna "Tecomex  Forensics Ltd" domin yayi aikin gina musu fasahar tsaro na na'ura mai kwakwalwa a cikin mota ta yanda ba za'a iya yiwa motar kutse (hacking) ba, wacce zata iya tuka kanta taje ko'ina ta dawo ba tare da direba ba.

 Kusan watanni 10 da suka gabata wani Lokaci da yamma Dr Idris Ahmed ya kirani a waya lokacin ya dauki lokaci mai tsawo bai hau online ba, yake sanar dani kwangilar da wannan kamfanin kera motoci ya bashi, amma yace min kada na sanar da kowa, a Kasar turai fa jama'a, 'dan Nigeria suka nema suka bashi wannan kwangila saboda ilminsa a harkon samar da tsaro wa na'ura mai Kwakwalwa

Allah Ya jikan Malam Albaniy Zaria Masanin na'ura mai kwakwalwa, wani lokaci Malam Albaniy Zaria yana gabatar da Lecture mai taken DUNIYAR ALJANU DA SHAIDANU lokacin da Malam yazo yana bayanin kwarewar da Aljanu suke dashi akan fasaha, sai da Malam Albaniy ya kawo bayanin cewa yanzu haka turawa suna nan suna tunanin yadda zasu kirkiri wata mota mai fasaha ta yadda zata iya tuka kanta, a aiketa taje ta dawo ba tare da direba ba, tsarki ya tabbata ga Allah, wato kamar Malam Albaniy Zaria yana mana ishara Dr. Idris Ahmed ne, yau abin ya zama gaskiya, Allah Ka jikan Malam Albaniy Zaria 

Muna alfahari da kai Maigidana Dr Idris Ahmed Allah Ya kara maka fasaha
Muna fatan Allah Ya sa duniya ta cigaba da amfana da rayuwarka. Amin.
Daga Datti Assalafiy.


No comments:

Post a Comment