Monday, 18 February 2019

Duk wanda ya saci akwatin zabe ya yi a bakin ransa>>Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana cewa duk dan siyasar da ya saka 'yan daba su sa ci akwatin zabe suna yi ne a bakin rayuwarsu.


Shugaban dai ya bayyana haka a wani taron gaggawa na shugabanni da masu ruwa da tsaki na jam'iyyar APC da ya gudana a babbar sakatariyar jam'iyyar dake Abuja babban birnin kasar.

Shugaban ya ce tuni ya sanar da jami'an tsaron kasar da su hukunta duk barawon akwatin da suka damke a ranar zabe ta hanyar nuna "rashin tausayi."


Bayan haka ya kuma ce dole ne bayan an kammala zaben hukumar zabe mai zaman kanta a kasar ta fito ta yi cikakken bayani a kan dalilin dage zaben kasar da ta yi.

Shugaba Buhari ya bayyana cewa dage zaben da hukumar ta yi ya nuna matukar gazawar hukumar.

Ya kara da cewa: "Ba na sa ran wani ya kawo wata hayaniya, na tattauna da jami'an tsaro da sojoji, sun riga da sun binciko wuraren da za a iya tayar da rikici, su zama cikin shiri domin zuwa irin wadannan wurare.

"Kuma mun riga munyi wa jami'an tsaro shirye-shirye, kuma kasa ta yi masu tanadin kudade iya gwargwado, duk wanda ya ce zai saci akwatin zabe ko ya jagoranci 'yan daba domin kawo rikici, wata kila wannan ce keta doka ta karshe da zai yi a rayuwarsa.

"Na ba jami'an tsaro da sojoji umarni da kada su ji tausayi, ba za mu so a zarge mu da magudin zabe ba, ina so a mututunta 'yan Najeriya, a bar su su zabi wanda suke so a ko wace jam'iyya yake.

"Bana jin tsoron haka, na zagaye jihohin Najeriya 36 har da Abuja, ina ganin na samu goyon baya a duk fadin kasar.

"A bisa wannan dalili ne yasa zan gargadi duk wanda yake gani yana da karfi a yankinsa domin jagorantar yan 'yan daba domin satar akwatuna ko kuma tayar da hayaniya a wurin zabe, zai yi hakan ne a bakin ransa," in ji Shugaba Buhari.

A ranar 16 ga watan Fabrairun 2019 ne hukumar zaben ta dage babban zabenta sa'o'i kalilan kafin fara zaben.

Hakan ya jawo ce-ce-ku-ce daga wasu daga cikin 'yan Najeriyar da jam'iyyun siyasa bisa dage wannan zabe sa'oi kadan kafin a fara gudanar da shi
BBChausa.

No comments:

Post a Comment