Monday, 11 February 2019

Duk 'yan Kannywood masu yin APC dan kudu suke yi>>Adam A. Zango

Bayan canja shekar siyasa da tauraron fina-finan Hausa kuma mawaki, Adam A. Zango yayi an yi ta cece-kuce, Adamun ya mayar da martani akan sukar da ake mai akan canja sheka da yayi daga APC zuwa PDP, yace cin fuska, hantara da rashin sanin muhimmancin shine yasa ya fita daga APC.A wani faifan bidiyo da ya fitar ta dandalinshi na sada zumunta, Adamu yace ya kamata masu zaginshi dan ya canja jam'iyya su sani cewa siyasa fa ba addini bace, kasuwancine wanda zaka zuba kudinka dan ka samu riba.

Idan kaga ba zaka samu riba ba sai ka canja inda kake tunanin samun nasara.

Yace a lokacin yana APC babu irin gudummuwar da be bayar ba amma a banza, haka za'a rika kiran wasu ana basu miliyoyin kudi, an yi ba daya ba ba biyu ba, abin har yana so ya zama da hassada a ciki.

Adam yace akwai lokacin da yana kan dandamali yana wasa haka jami'an tsaro zasu zo su tureshi gefe a kawo wanda yasan ya fisu bayar da gummuwa a tafiyar APC ace su yi wasa, ya kara da cewa kai wani lokacin ma idan suka je shiga guri hanashi shiga ake sai wani daga cikin wanda suke tare ya saka baki dan haka yaga bazai iya ba.

Akan masu cewa kudi aka bashi, adam yace duk 'yan Kannywood dake APC da kudi suke yin APC sai shine dan yayi dan kudi sai a zageshi?

Ya kara da cewa, ba dan kudi yake yi ba, kiranshi aka yi aka bashi jakadan yakin neman zaben na Atiku akace yayi amfani da tunaninshi dan fito da yanda zai taimaka wajan tafiyar ya kai za'a bashi dama yayi.

Yace ya ji wasu abokan sana'arshi na cewa wai an bashi kudi kaza da kaza, to fa idan basu daina ba shima zai fito ya fallasasu dan yasansu sun sanshi.

No comments:

Post a Comment