Monday, 11 February 2019

Fadar shugaban kasa ta aika wakilanta jihar Taraba dan yin gaisuwar jama'ar da suka rasu a wajan yakin neman zaben Buhari

A jiya, Lahadi ne fadar shugaban kasa ta wakilta sakataren shugaban kasa, Boss Mustafa da me magana da yawun shugaban kasar, Femi Adesina da shugaban hukumar habaka fasar labarai, Dr. Isah Ali Fantami da gwamnan Adamawa, Muhammad Umar Jibrilla, Bindow dadai sauransu dan yin gaisuwar jama'ar da suka rasu yayin yakin neman zaben shugaban kasa, Muhammadu Buhari a jihar Taraba.Tawagar ta je fadar mulkin jihar Taraba inda ta mika sakon ta'aziyya ga gwamna Darius Ishaku da kuma iyalan mamatan, shugaban ya tabbatar da cewa wanda suka rasun basu yi mutuwar banza ba dan shugaban zai ci gaba da gudanar da ayyukan inganta rayuwar al'umma.

Kimanin mutane 8 ne aka ruwaito cewa sun mutu sanadiyyar turmitsutsu a wajan yakin neman zaben da Buhari yayi a jihar.No comments:

Post a Comment