Monday, 11 February 2019

Gasar Firimiya: Liverpool ta doke Bournemouth 3-0: Arsenal ta doke Huddersfield 2-1

A gasar English Premier League da aka kara tsakanin Liverpool da Bournemouth, Ƙungiyar Liverpool ta doke Bournemouth da ci 3-0


A yayinda ake mako na 26 Liverpool ta jefa kwallaye uku a ragar Bournemouth a mintuna na 24 wanda Sadio Mane ya jefa sai kuma a minti na 34 ta Georginio Wijnaldum da kuma na minti 48 wanda dan kasar Misira Muhammed Salah ya jefa.

Liverpool nada maki 65 a matsayin ta biyu inda Manchester City ke matsayi na daya da maki 65. Ƙungiyar Bournemouth ta kasance mai maki 33 inda ta kasance ta 11 a teburin.

Arsenal wacce ke kokarin zuwa na huɗu ta ja daga da Huddersfield Town inda aka tashi 2-1

A wasan da Mesut Özil bai kasance cikin yan wasa 18, Alex lwobi ya jefa kwallo raga a minti na 16; a yayinda Alexander Lacazette ya ƙara daya a minti na 44. Ita kuwa Hunderfield Town ta jefa kwallo daya tilo ne ta ɗan wasa Sead Kolasinac a minti na 90+3.

Arsenal wacce ta kasance ta 6 da maki 50 ta bar Hunderfield Town ta baya da maki 11.


No comments:

Post a Comment