Sunday, 17 February 2019

Girona ta ci Madrid a Santiago Bernabeu

Real Madrid ta yi rashin nasara a hannun Girona da ci 2-1 a wasan mako na 24 a gasar cin kofin La Liga da suka kara a ranar Lahadi a Santiago Bernabeu.


Real ce ta fara cin kwallo ta hannun Casemiro minti 25 da fara tamaula, kuma haka aka je hutu Madrid na da kwallo daya.

Bayan da aka dawo ne Girona ta farke ta hannun Cristhian Stuani a bugun fenariti, sannan Cristian Portugues ya kara na biyu saura minti 15 a tashi daga karawar.

Madrid ta karasa wasan da 'yan kwallo 10 a cikin fili, bayan da aka bai wa kyaftin din ta Sergio Ramos jan kati daf da za a tashi daga fafatawar.

Da wannan sakamakon Real Madrid ta koma ta uku a kan teburin La Liga da maki 45, inda Atletico ce ta biyu da maki 47, Barcelona na nan a matakinta na daya da maki 54.


Real za ta ziyarci Levante ranar 24 ga watan Fabrairu a wasan mako na 25 a gasar La Liga, sannan ta karbi bakuncin Barcelona a wasa na biyu na daf da karshe Copa del Rey ranar 27 ga watan Fabrairu.

Barcelona da Real Madrid sun tashi 1-1 a wasan farko na daf da karshe a Copa del Rey da suka yi ranar 6 ga watan Fabrairu a Nou Camp.

Haka kuma a ranar 2 ga watan Maris ne Real Madrid za ta karbi bakuncin Barcelona a gasar La Liga wasan mako na 26 a Santiago Bernabeu.

A wasan farko da kungiyoyin biyu suka kara a La Liga, Barcelona ce ta yi nasara da ci 5-1 a ranar 28 ga watan Oktoban, 2018 a Nou Camp.

Kwana daya da yin wasan ne Madrid ta kori kocinta Julen Lopetegui ta nada Santiago Solari rikon kwarya daga baya ta ba shi wuka da naman jan ragamar kungiyar.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment