Saturday, 16 February 2019

Gwamnatin jihar Taraba ta dawo da mutuminnan da ta kora daga aiki bayan da matarshi ta rasu wajan yakin neman zaben Buhari aikinshi

Mutuminnan na jihar Taraba wanda matarshi ta rasu a wajan yakin neman zaben shugaban kasa, Muhamadu Buhari a jihar, watau Alhaji Haruna Kawuwa wanda sanadiyyar haka gwamnatin jihar ta koreshi daga aiki, yanzu dai an mayar dashi bakin aikinshi.A cikin takardar dawo dashi aiki da akayi an shaidamai cewa bayan lamarin da ya faru na mutuwar mutane wanda hadda matarshi a wajan yakin neman zaben shugaban kasa, Muhammadu Buhari a jihar, shugaba  kasar ya aike da tawagar gaisuwa wadda sakataren gwamnatin tarayya ya jagoranta zuwa jihar.

Dalilin haka gwamna Darius Ishaku ya sake duba korar da aka mai daga aiki, ya kuma bukaci da a dawo dashi bakin aiki.
No comments:

Post a Comment