Monday, 18 February 2019

GWARZON MALAMAI ABIN KOYI

1. Sheikh Dr Sani Umar Rijiyar Lemo
2. Dr Ahmad Ibrahim BUK
Duk Malamin da ya dauki salon da'awa irin na Dr Sani ba wani mutum komai shegantakar sa da zaiyi masa iskanci ko yayi masa rashin kunya.


Sune Malaman da ba ruwansu da shiga sabgar masu mulki, basa zuwa office din Gwamna neman kwangila ko neman shiga ko fadanci tsakanin su da mawadata ko masu mulki sai fadar Gaskiya. In sunga dama su dauka, in sunqi dauka oho, su dai sun sauke nauyin da yake kansu.

Malamai ne da basu da kwadayi da tumasanci, sun riqe girmansu da mutuncinsu da malintar su wadda Allah S.W.A.Ya ba su. Basa shiga abin da ba ruwansu, sun fi mayar dakai wajen karantarwa da wayar da kan mutane. Suna girmama kowa su kullum burinsu dalibai su tsaya suyi karatu.

Allah Ya taimaki Dr Ahmad da Dr Sani, Yayi musu jagora. Allah Ya gyara malaman mu Ya dora su akan hanya madaidaiciya damu gaba daya.
Daga Usman Albani Abu Abdilrahman.


No comments:

Post a Comment