Tuesday, 12 February 2019

Hajara Usman Ta Bi Sahun Adam A. Zango A Tafiyar Atiku

Da alama komawar tauraron fina-finan Hausa kuma mawaki, Adam A. Zango jam'iyyar PDP zata ja jarumai da yawa daga cikin masana'antar dan kuwa bayan Maryam Gidado an sake samun Hajara Usman itama ta bi sahun Zangon.


Ga abinda tace kamar yanda Rariya ta ruwaito:

"Da na samu sakon Adam A. Zango, akan cewa duk masoyan sa su zabi Atiku, duk da soyayya ta da Buhari, sai na ji na hakura, domin na biyo Adamu. Adam A. Zango shine mutumin da ya fi kowa halacci da daraja na gaba da shi a kaf cukin kannywood, sannan ya dauke ni tamkar mahaifiyar sa na gaskiya, ni ma a haka nake kallon sa matsayin da na na cikina, Don haka duk inda ya koma ni ma nan zan koma".


No comments:

Post a Comment