Monday, 18 February 2019

Hukumar 'yansanda zata yi bincike akan wannan hoton

Bayan da wani ya jawo hankalin hukumar 'yansanda akan wannan hoton dake nuna wasu jami'ansu da suka yi inkiyar 4+4 dake nuna alamar goyon baya ga shugaban kasa, Muhammadu Buhari wadda yace be kamata ba domin jami'an 'yansanda na kowane ya kamata su nesanta kansu da siyasa. Shugaban 'yansandan ya sa a yi bincike akan hoton.Hukumar 'yansandan ta shafinta na sada zumunta ta tabbatar da cewa shugaban 'yansandan yasa a yi bincike akan sahihancin hoton sannan kuma za'a sanar da matakin da aka dauka ga jama'a.

No comments:

Post a Comment