Monday, 18 February 2019

INEC ta baiwa jam'iyyu damar ci gaba da yakin neman zabe

Hukumar zabe me zaman kanta, INEC ta baiwa jam'iyyun siyasa damar ci gaba da gudanar da yakin neman zabe daga nan zuwa daren ranar Alhamis ta kuma ce kafafen watsa labarai zasu iya ci gaba da yin tallar 'yan siyasa har zuwa ranar Alhamis din.INEC din ta sanar da hakanne a shafinta na sada zumunta bayan taron da ta yi yau.

Ta kara da cewa a gobe, Talata zata fitar da karin bayanai akan dage zabe.


No comments:

Post a Comment