Saturday, 16 February 2019

INEC ta dage manyan zabukan Najeriya

Hukumar zaben ta Najeriya ta ce ta dage zaben ne zuwa ranar 23 ga watan Fabrairu.


Da yake sanar da matsayin hukumar ranar Asabar da kusan asubahi, shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya kara da cewa an dage zaben gwamnoni zuwa ranar tara ga watan Maris.

Farfesa Yakubu ya ce sun dauki matakin ne sakamakon matsalolin rashin kai kayan zabe a wasu yankunan kasar a kan lokaci.


A cewarsa, "Hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya ta gana ranar Juma'a, 15 ga watan Fabrairu inda ta sake nazari kan shiriye-shiryenta na zaben shekarar 2019, don haka an dage zaben da za a yi ranar Asabar 16 ga watan Fabairu zuwa ranar Asabar, 23 ga watan Fabrairu. Kazalika, za a gudanar da zaben gwamnoni ranar tara ga watan Maris."

Da ma dai rahotanni daga sassan kasar da dama sun bayyana cewa ba a kai kayan aikin zaben ba har cikin dare, abin da ya sa wasu 'yan siyasa zargin cewa ana shirya magudi.

Masu sharhi na ganin wannan mataki zai kara tabbatar da zargin da wasu suka yi ta yi cewa hukumar ba ta shirya ba, amma ta rinka musanta hakan.

Hakan kuma ka iya haddasa rashin jin dadi a tsakanin wasu 'yan kasar ganin yadda da ma suka yi tattaki zuwa yankunansu domin kada kuri'a.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment