Friday, 22 February 2019

INEC ta fadi ranar da zata bayyana wanda ya lashe zaben shugaban kasa

Hukumar zabe me zaman kanta, INEC ta bayyana ranar da zata fadi sakamakon zaben shugaban kasa da za'ayi gobe, Asabar idan Allah ya kaimu, INEC tace zata bayyana sakamakon zabenne daidai da lokacin da aka bayyana na shekarar 2015 duk da cewa yawan masu zabe da kuma girman takardar sakamakon zaben sun karu.Shugaban INEC din Farfesa, Mahmood Yakubu ya tabbatar da cewa sun kammala shirya na'urorin zaben da za'a yi amfani dasu gobe ya kuma tabbatar wa da 'yan jarida cewa zasu yi aiki tukuru dan ganin basu bar 'yan Najeriya suna ta jiran sakamakon zaben ba.

Wannan jawabi na shugaban INEC na nuni da cewa ranar Laraba me zuwa kenan zasu bayyana wanda ya ci zaben shugaban kasar saboda a zaben 2015 ma da aka yi shi a ranar Asabar sai ranar Laraba ne aka bayyana wanda yayi nasara.

No comments:

Post a Comment