Tuesday, 12 February 2019

Izgili Ga Sunnah Da Ma'abotanta Halaka Ne Duniya Da Lahira.

Kar ka dubi su wane aka soka, ko kuma adawarka gare su, a'a ka tsaya ka dubi sunnar wa aka soka?! Shiriyar wa aka yi wa izgili da cin mutunci?!. 


Wannan addini na Allah ne, kuma wajibi ne akan dukkan wani musulmi ya nuna damuwarsa da bacin ransa idan an soki addinin ko an bata wani abu na shiriyarsa.

Sunnar Allah a bayan kasa tabbatacciya ta nuna Allah baya kyale duk wanda ya taba shiriyar Manzon Allah a duniya da lahira, sai in ya tuba.

Allah Ka wulakanta duk wanda yake wulakantar sunnar ManzonKa.
Muhammad Rabiu Rijiyar Lemo.
Sarauniya.No comments:

Post a Comment