Wednesday, 27 February 2019

Jawabin murnar cin zaben shugaba Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi magoya bayansa jawabi bayan hukumar zaben kasar ta tabbatar da shi a matsayin wanda ya lashe zaben 2019 ranar Laraba.


Da farko shugaban ya gode wa Ubangiji "wanda ya nuna wa 'yan Najeriya wannan rana a tarihin dimokradiyyar kasar nan da kuma nasarar jam'iyyar APC."

Daga nan ya yi godiya ga miliyoyin 'yan Najeriya da suka sake zabensa sabon wa'adi na biyu.

"Ina alfahari da kuma godiya da kuka yi min wannan alkalanci da yadda kuka kara ba ni wata damar," in ji shi.


Ya kuma yi godiya ga Asiwaju Bola Tinubu yadda ya jagorancin kwamitin yakin neman zabensa.

"Ina kuma godiya ga Shugaban Jam'iyyar APC Adams Oshiomhole da Darakta Janar na kamfenmu Rotimi Amaechi da sauran jagorori da kungiyoyin yakin neman zabenmu," in ji shi.

Ya kuma gode wa sauran wadanda suka taimaka da kuma masu sanya ido na ciki da wajen kasar.

Ya yi alkawarin gurfanar da mutanen da aka kama bisa zargin aikata laifukan zabe. Ya kuma bayyana bakin cikinsa game da yadda wasu suka rasa rayukansu lokacin zaben."Jami'an tsaro za su dukufa wajen kare kuri'u a zabuka masu zuwa. Ina kuma yaba wa jami'an tsaro kan yadda suka yi aiki tukuru lokacin zaben."

Ya kuma ja kunnen magoya bayansa kan kada su muzanta wa 'yan adawa. "Nasara da muka samu ta gamsar da mu, ta biya mu," in ji shi. A karshe ya ce sabuwar gwamnatinsa za ta dukufa wajen tabbatar da tsaro da tattalin arziki da kuma yaki da cin hanci da rashawa.

Ya yi kuma alkawarin ci gaba da aiki tukuru don ganin an magance matsaloli da karfafa hadin kan kasa.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment