Monday, 11 February 2019

Jose Mourinho ya samu aikin yi

Jose Mourinho zai yi sharhin wasannin tamaula kan wasannin gasar cin kofin Zakarun Turai Russia Today.


Karo na biyu kenan da zai yi aikin da gidan talabijin din Rasha, bayan wanda ya yi a lokacin gasar cin kofin duniya da kasar ta karbi bakunci a 2018.

Gidan talabijin din ya sanar cewar Mourinho zai dunga yi masa sharhin wasannin gasar cin kofin zakarun Turai da manyan batutuwan da suka shafi tamaula a duniya.

Tsohon kocin na Manchester United zai fara sharhi kan wasannin Champions League da za a fara a ranar Talata da wadan da za a yi Laraba har zuwa karawar karshen gasar.

Mourinho ya kai United wasan zagaye na biyu a gasar zakarun Turai, daga baya ta sallame shi, bayan da ya kasa taka rawar gani ta kuma nada kocin rikon kwarya Ole Gunnar Solskjaer.

Tun bayan da Solskjaer ya karbi aiki a Old Trafford ya ja ragamar karawa 11, inda ya ci wasa 10a canjaras daya.
BBChausa.


No comments:

Post a Comment