Tuesday, 12 February 2019

Juventus ta sanya hannu da Ramsey

Kungiyar kwallon kafa ta kasar Italiya Juventus ta amince da sayen dan wasa Aaron Ramsey dake taka leda a kungiyar Arsenal ta Ingila wanda kwantiraginsa za ta kare a a kakar wasanni ta bana.


Kungiyar ta fadi cewa, za ta dinga biyan dan wasan kudi har Yuro dubu 400,000 a kowanne mako.

Bayan 'yan wasa irin su Kingsley Coman, Sami Khedira, Dani Alves da Emre Can a yanzu Juventus ta sake samun wani sabon dan wasan.

Ramsey dake taka leda a Arsenal ya buga wasanni 259 a cikin shekaru 11 inda ya jefa kwallaye 61.


No comments:

Post a Comment