Friday, 15 February 2019

Juventus za ta ajiye kudi da dan wasanta domin sayen Salah

Rahotanni daga Italiya na cewa, kungiyar kwallon kafa ta Juventus ta bayyana shirinta na bai wa Liverpool Pam miliyan 44 da kuma karin dan wasanta Paulo Dybala duk dai da nufin sayar ma ta da Mohamed Salah.Jaridar Tuttosport da ta wallafa labarin a shafinta na farko ta ce, Juventus da gaske take wajen kulla cinikin sayen Salah dan asalin Masar kuma gwarzon dan kwallon Afrika.

Dan wasan ya kulla sabon kwantiragin shekaru biyar da Liverpool a cikin watan Julin bara, kuma sharuddan kwantiragin ba su kunshi batun sakin sa ba.

Salah ya ci wa Liverpool kwallaye 20 a cikin wannan kakar, yayin da Dybala ya ci wa Juventus kwallaye takwas a wasanni 33 da ya buga ma ta kawo yanzu.
RFIhausa.

No comments:

Post a Comment