Wednesday, 20 February 2019

Ka janye kalamanka sannan ka nemi afuwarmu>>Buratai ya gargadi Atiku akan cewa da yayi kada su bi umarnin Buhari na harbin barayin akwatin zabe

Shugaban rundunar sojin Najeriya, Janar Tukur Yusuf Buratai ya bayyana kalaman dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar da yace su yi watsi da umarnin shugaban kasa, Muhammadu Buhari na harbe masu satar akwati da cewa abin takaicine.Buratai yace be kamata ace wadannan kalamai sun fito daga bakin Atikun ba kasancewarshi ya taba zama mutum na biyu a kasarnan sannan kuma yasan cewa Sojin Najeriya umarnin shugaban kasane suke bi wanda shine kwamandansu amma yace wai su yi watsi da umarnin da ya basu.

Buratai yace aikinsune su aiwatar da umarnin shugaban kasa ba tare da tantatama ba kuma kada wani dan siyasa yayi tunain zai gwadasu dan ba zasu yi wata-wata ba wajan bin umarnin da shugaban kasa ya basu ba.

Ya bukaci Atikun da ya fito ya janye kalaman nashi sannan kuma ya nemi afuwar sojan bisa yunkurin kiran da ya musu Na cewa su yi watsi da umarnin da aka samar da su musamman dan su bi.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa, Buratai yayi wannan kalamine a wajan wani taron sojojin da ya wakana kuma duk da cewa be ambaci sunan Atiku ba amma dukkan alamu sun nuna cewa dashi yake.

Sannan Buratai din yace za'a janye jami'an sojin da aka baiwa tsaffin janar-janar musamman wadanda suka shiga harkar siyasa dan ba za'a yadda Sojoji su rika rakiyar dan siyasa ba sannan duk sojan dake da muradin siyasa yayi gaggawar ajiye aikinshi nan da 22 ga watan Fabrairu.

No comments:

Post a Comment