Monday, 11 February 2019

Kada ku siyasantar da kungiyar Izala>>Sakon Sheikh Gumi ga malaman Izala

"Kungiyar Izala kungiya ce ta wa'azi da koyar da mutane addini a birane da kauyuka, dan haka kada wannan kungiya ta sake ta karbi kudi wurin wasu 'yan takara akan cewa za su sa mabiya su zabe su.


"Mulki na Allah ne kuma shine yake badawa ga duk wanda yake so, babu wanda zai iya ba wasu mulki saidai ya yaudare su a banza, dan haka wannan kungiya ta ji tsoron Allah kada ta jefa kanta cikin hallaka, sannna ta sani Allah zai tambaye ta akan abubuwan da ta gabatar ranar gobe kiyama.

"Ku kuma mutanen gari ga zabe nan ya taho ku yi Istikhara akan zaben shugaba na kwarai wanda zai iya yi muku abubuwan da suka dace da ku a addinin ku da rayuwar ku.

"Kada ku yi fada da junanku a ranakun zabe ku zama masu tausayawa junanku kuma ku zabi wanda kuke so ba wanda aka tirsasa ku akan ku zabe shi ba.

"Allah ya sa a yi zabe lafiya kuma a gama lafiya."

Wannan sakon Sheikh Dr. Ahmad Gumi ne zuwa ga Al'ummar Nijeriya.
Rariya.


No comments:

Post a Comment