Saturday, 9 February 2019

Kalaman El-Rufa'i Yunkuri Ne Na Bata Sunan Najeriya>>Sule Lamido

Tsohon ministan harkokin waje na Najeriya Alhaji Sule Lamido, kuma tsohon gwamnan jihar Jigawa Kuma, ya ce a tsari na Diplomasiyyar kasa da kasa, kalaman gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufa'i yunkuri ne na bata sunan Najeriya a idon duniya.
Alhaji Sule Lamido ya yi wannan bayanin ne a wata hira da wakilin Muryar Amurka, Mahmud Ibrahim Kwari, biyo bayan kalaman da gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufa’i yayi na cewa duk wasu wakilai ko kungiyoyin kasashen waje da za su so yin katsalanda a harkokin zaben da za yi ranar 16 ga watan Fabarairu, “za a maida gawarwakin su kasashen su.”

Tsohon ministan ya ce, gwamnan na magana ne kawai don a san da zaman shi, kuma don yana amfani da girman mukamin sa, amma baya da hurumin yin wadannan kalaman a matsayin sa na gwamna kuma hakan na muzanta Najeriya ne kawai a idon duniya.

Alhaji Sule Lamido ya kuma ce, lafazin da gwamnan yayi ba zai yi wani tasiri ba a zaben da za a yi ta fuskar diflomasiyya. Ya kuma kara tunatar da jama’a akan yadda wasu wakilan kasashen waje suka yi ta kai-da-komo don tabbatar da an yi zaben gaskiya da adalci a shekarar 2015, kuma gwamna El-Rufa'i a wancan karon ya yaba da kokarin kasashen.

A siyasance kuma tsohon ministan ya ce wannan “kada bula ce kawai yake yi.”
VOAhausa.

No comments:

Post a Comment