Saturday, 9 February 2019

Kalli abinda matar mataimakin shugaban kasa tayi wa wani gurgu da ake ta yaba mata

A yaune aka yi tattaki dan nuna goyon baya ga shugaban kasa, Muhammadu Buhari a babban birnin tarayya, Abuja inda matar mataimakin shugaban kasa, Dolapo Osinbajo ta jagoranci lamarin. Dolapo ta yi wani abin sam barka da ya matukar birge mutane a wajan.A lokacin tattakin akwai wani gurgu da ta gani yana rarrafawa, ashe abin na ranta, bayan da ta koma fadar shugaban kasa sai gashi ta aikomai da keken guragu sabo fil.

Gurgun ya nuna farin ciki sosai inda da dama jama'ar dake gurin suma suka yi sambarka.


No comments:

Post a Comment