Sunday, 10 February 2019

Kama barayin gwamnatine aikin gwamnatina>>Shugaba Buhari

Shugaban kasa,Muhammadu Buhari ya tabbatar da cewa aikin gwamnatinshi shine kama barayin gwamnati da suka sace dukiyar kasa.Shugaban ya tabbatar da hakane a wajan yakin neman zaben da yaje jihar Legas jiya, Asabar, yace duk wanda aka baiwa kayan gwamnati to hakkinshine ya ga cewa yayi aiki yanda ya kamata ya kuma bayar da ba'asin yanda ya gudanar da aikinshi.

Yace duk wanda suka dauke dukiyar gwamnati kuma basu dawo da ita ba to aikin gwamnatinshine su kamasu su kwace dukiyar sannan su mikawa kotu ta hukuntasu.

No comments:

Post a Comment