Thursday, 14 February 2019

Kamin a samu masoyin shugaba Buhari irin Hadiza Gabon sai an tona>>Karahta dalili

Tauraruwar fina-finan Hausa, Hadiza Gabon ta kara jaddada soyayyar ta ga shugaban kasa,Muhammadu Buhari a zabe me zuwa, abokin aikinta, Tijjani Asase ya bayyana wani sirri dake bayyana irin soyayyar da Hadiza kewa Buharin wadda sai an bincika kamin a samo masuwa shugaban irin wannan soyayya.Hadizar ta saka hotuna masu nuna cewa tana tare da shugaban kasar.

Tijjani Asasase ya bayyana yanda Hadizar tana kasar Nijar a zaben 2015 kuma an kulle boda taso ta dawo Najeriya dan ta sakawa Buhari kuri'a amma akace a'a, yace har kuka sai da ta yi daga baya dai aka samu aka shigo da itaa Najeriya.

Ga cikakken jawabin Tijjani.

'Wannan ita ce Hadiza Aliyu Gabon Babbar jaruma a masa na antar fim, din Hausa ni na shayda,a arewa nan ta mu, samu mace mai san Baba Bahari kamar Hadiza, aikine natina wata waka ta su Nazifi da Ali jita wai ita,Dalili na, nafadin haka, shine zaben Bahari na farko muna kasar Nijar muna aiki,Hadiza tace wlh sai ta dawo Najeriya ta zabi Baba. alokaci anrufe Boda hankalinta ya tashi harda kuka,wlh harsai da aka samu ma'aykatan na can da na nan daker a kabarta, ta Shigo kasar nan. kuma Bazaka ta ba ganin ta a wajan da ake karbar na goro ba, bayan anci Zabe ko kaga hotanta agun da akeyi da Bahari, kuma har kudin ta 'ta ke kashewa kan azabi Bahari. yanzuma gashi ya kamata tabar kasarnan dan ci gabanta taki ta tsaya sai ta zabi Baba Allah yasaka miki dije.'

No comments:

Post a Comment