Thursday, 14 February 2019

Karanta abinda Adam A. Zango yace akan General BMB

Tauraron fina-finan Hausa kuma mawaki, Adam A. Zango ya saka hoton abokin aikinshi, Bello Muhammad Bello, General BMB dake goyon bayan shugabannkasa, Muhammadu Buhari inda ya bayyana cewa dan uwanshine, kuma yana jan hankalin mutane cewa kowa ya zabi ra'ayinshi.Adamun ya kara da jawo hankalin cewa, kada a yo tashin hankali akan wani dan siyasa, ga abinda ya rubuta kamar haka:

He is my brother no matter what! Ka zabi ra'ayinka in zabi ra'ayina. Bayan mu dawo sana'armu muci gaba daga inda muka tsaya! HAKA AKE SIYASA....
.
KARKA DAKI KO KA KASHE DAN UWANKA DON WANI GWAMNA, SANATA KO SHUGABAN KASA.
.
DON ALLAH MU KIYAYE MUYI ZABE CIKIN KWANCIYAR HANKALI.
.
ALLAH YA BAIWA MAI RABO SA'A KUMA YA ZABA MANA MAFI ALKHAIRI!
.
AMMA NI DAI ZABI NA AHINE WAZIRIN ADAMAWA ALH ATIKU ABUBAKAR!


No comments:

Post a Comment