Tuesday, 26 February 2019

Karanta abinda Sanata Dini Melaye yace akan faduwar ubangidanshi, Sanata Saraki

Kakakin majalisar dattijai, Sanata Bukola Saraki na daya daga cikin 'yan siyasar kasarnan da guguwar zaben 2019 ta yi waje dasu, babban na hannun damarshi, Sanata Dino Melaye shi ya tsallake ya kuma bayayyana matsayinshi akan faduwar Sarakin.Dino Melaye ya yabi Sanata Saraki a shafinshi na Twitter inda ya bayyanashi a matsayin gwarzon dimokradiyya, me kishin kasa, da kuma kare mutunci ta, yace duk wani tuggu da za'a shiryawa Sarakin na dan lokaci ne da zai wuce, yace, har yanzu kai me gidanane, dan uwa kuma aboki, ina sonka.


No comments:

Post a Comment