Sunday, 17 February 2019

Karanta martanin Ronaldo kan siyen Salah da Juventus zata yi

Tauraron dan kwallon kasar Portugal me bugawa kungiyar Juventus wasa, Cristiano Ronaldo ya goyi bayan kungiyar tashi a kokarin saye Mohamed Salah daga Liverpool.Sky News ta ruwaito cewa, Ronaldon ya nuna amincewa da sayen Salah dinne a yayinda ake tsammanin zai nuna adawa da hakan ganin cewa kamar kishiyane za'a samar mishi.

Juventus dai tana kokarin bayar da dan wasanta Dybala hadi da Fan miliyan 43 dan ganin Liverpool din ta sakar mata Salah a karshen kakar wasa.

No comments:

Post a Comment