Sunday, 17 February 2019

Kasashen Duniya sun gamsu da dage zaben Najeriya

Kungiyoyin kasashen duniya da ke sa ido kan zaben Nejeriya na 2019 da suka hada da Majalisar Dinkin Duniya sun ce, sun gamsu da uzurin da Hukumar Zaben Kasar ta bayar na dage zaben shugaban kasar zuwa makon gobe.A cikin wata sanarwar hadin guiwa da suka fitar, kungiyoyin da suka hada da Majalisar Dinkin Duniya da Kungiyar Kasashen Afrika, AU da Kungiyar Tarayyar Turai, EU da Cibiyar Bunksa Demokradiya ta NDI mai cibiya a Amurka sun ce, sun gamsu da dalilan hukumar INEC da ta ce, ta dage zaben ne saboda matsalolin isar da kayayyakin kada kuri'u.

Kungiyoyin sun bukaci daukacin al’ummar Najeriya da su kwantar da hankulansu duk da cewa, wannan matakin dage zaben a kurarren lokaci bai yi musu dadi ba.

Sanarwar wadda sashen Hausa na RFI ya samu kwafinta, ta kuma bukaci hukumar zaben kasar, wato INEC da ta yi amfani da wannan dagewar don kammala kintsawarta domin gujewa sake dage zaben nan gaba.

Har ila yau, kungiyoyin sun bukaci INEC da ta ci gaba da sanar da jama’a duk wani hali da ake ciki dangane da shirye-shiryen zaben na shugaban kasa da na ‘yan Majalisu.

Daga karshe dai, sanarwar kungiyoyin ta ce, suna goyon bayan Najeriya dari bisa dari wajen gudanar da sahihin zabe.
RFIhausa.

No comments:

Post a Comment