Tuesday, 26 February 2019

Komai yayi farko zai karshe: Kalli hotunan Sanata Bukola Saraki a majalisa yau

Kakakin majalisar dattijai, Sanata Bukola Saraki kenan wanda ya fadi zabenshi a zaben shugaban kasa dana 'yan majalisu da ya gudana ranar Asabar din da ta gabata, yau, Talata a zaman majalisar na farko tun bayan zabe.Majalisar dai bata samu yin zaman ba saboda ba'a samun yawan 'yan majalisar da doka ta amince a zauna ba, dan hanaka aka daga zaman. Masu iya magana na cewa, duk abinda ya baka tsoro wataran zai baka tausai haka duk abinda ya baka tausai wataran zai baka tsoro.

No comments:

Post a Comment