Wednesday, 13 February 2019

Kotu ta bayar da belin Babachir

Wata kotun Abuja ta bayar da belin tsohon sakataren gwamnatin tarayya Babachir David Lawal a ranar Laraba.


An ba da shi beli bayan ya shafe kusan sa'o'i 24 a hanun hukumar EFCC da ke yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya.

Tsohon Sakataren Gwamnatin Kasar Babachir David Lawal ya musanta zarge-zarge goma da hukumar EFCC ta gabatar a gaban kotu a kansa, inda cikin zargin da ake yi masa har da batun almundahana da kuma mallakar wasu kadarori ba bisa ka'ida ba.

Amma kotun a ranar Laraba ta bayar da belinsa da kuma wasu mutane biyu akan naira miliyan 50 da kuma wanda zai tsaya wa kowane a cikinsu.Kotun ta ce wanda zai tsaya ma kowane a cikinsu sai an tabbatar yana da gida a birnin tarayya Abuja da kuma shaidar biyan haraji na shekaru uku da suka gabata kuma ya kasance mazaunin Abuja.

Kotun ta bayar da umarnin cewa dole ne tsohon sakataren gwamnatin na tarayyar da sauran mutanen biyu su bayar da fasfonsu na tafiye tafiye domin cike sharuddan belin.

A watan Oktoban 2017 ne dai hukumar EFCC ta fara binciken tsohon sakataren gwamnatin Najeriyar bayan da shugaban kasar Muhammadu Buhari ya kori Babachir kuma ya kafa kwamiti domin gudunar da bincike kan zargin karkatar da kudaden da aka ware wa 'yan gudun hijira da rikicin Boko Haram ya daidaita.

Mista Babachir ya hallara a gaban kotu a safiyar Talata a Abuja babban birnin kasar inda daga baya kotu ta dage shari'ar zuwa Laraba.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment