Tuesday, 12 February 2019

Kotu ta dage shari'ar David Babachir Lawal:EFCC ta ci gaba da tsareshi

Wata kotu da ke birnin tarayya Abuja a Najeriya ta dage shari'ar tsohon sakataren gwamnatin tarayya a kasar Babacir Lawal zuwa Laraba.


Kotun dai ta bayar da umarnin cewa hukumar EFCC ta ci gaba da tsare Mista Lawal.

A lokacin sauraren karar, lauyan Mista Lawal ya bukaci da a bai wa wanda yake karewa beli.Amma lauyoyin EFCC da suka shigar da karar Babachir suka nemi kotu ta yi watsi da bukatar bayar da belinsa.


EFCC na zargin tsohon sakataren gwamnatin ne da laifin karkatar da kudaden da aka ware wa 'yan gudun hijira da rikicin Boko Haram ya daidaita.

Wannan zargin ne ya sa shugaba Muhammadu Buhari ya kore shi daga gwamnatinsa.


Tun bayan sauke Babachir daga mukaminsa, 'yan Najeriya ke ta ce-ce-ku-ce musamman kan tafiyar hawainiya da gwamnatin Buhari ke yi wajen gurfanar da Mista Lawal a gaban kotu.

Wannan shari'ar na zuwa ne kasa da mako daya a gudanar da babban zabe a kasar.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment