Thursday, 14 February 2019

Ku sake zabena ba zaku yi dana sani ba>>Buhari

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bukaci 'yan Najeriya da su sake zabenshi a zabe me zuwa inda ya tabbatar musu da cewa ba za su yi dana sanin hakan ba, shugaban ya bayyana hakane a wajan yakin neman zaben da yayi a babban birnin tarayya, Abuja.Shugaban ya kara da cewa a lokacin da suka karbi mulki, mai da ake sayar dashi akan sama da dala 100 ya fado zuwa tsakanin dala 37-38 amma daga baya sun yi nasara an fita daga wancan kangi.

Ya kara da cewa PDP ta kashe dala biliyan 16 wajan samar da wutar lantarki amma ba'a samu tsayayyar wuta ba.

Shugaban ya kara da cewa, ya cika alkawuran da ya dauka lokacin mulkinshi na farko, yace munsan yanda kasar take kamin ya hau mulki sannan anga irin kokarin da yayi na farfado da ita daga matsalar da ta shiga na tsaro da tattalin arziki da rashawa.

Saidai jam'iyyar PDP ta yiwa shugaban dariya akan yakin neman zaben nashi na Abuja inda tace jama'a basu fito ba da yawa wanda hakan yake nuna alamun gazawan sun kara da cewa jama'a sun daina fitowa tarbar Buhari wajan yakin neman zabenshi ne saboda sun gaji da mulkinshi.

No comments:

Post a Comment