Wednesday, 13 February 2019

Kudin gyaran Wuta dala biliyan 16: Obasanjo ya mayarwa da Buhari martani: Na riga na wanke kaina a cikin littafin dana rubuta idan baka iya karantawa kasa a karanta maka a kuma fassara maka a yaren da zaka fahimta

Bayan da rahotanni suka bayyana cewa shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya sha alwashin bincikar kudin da aka kashe akan gyaran wutar lantarki da suka kai dala biliyan 16 lokacin mulkin tsohon shugaban kasa, Obasanjo daga 1999 zuwa 2007, Obasanjon ya mayar wa da Buhari martani inda yace yayi mamakin fitowar wannan kalami daga bakin Buharin.A sanarwar da ya fitar ta hannun me bashi shawara kan kafofin watsa labarai, Kehinde Akinyemi, Obasanjo yace yaji abinda Buharin yace amma bai yi tunanin shugaba me cikakkiyar fahimtar abubuwa ba zai iya yin wannan magana.

Yace rahoton majalisar tarayya a wancan lokacin da binciken da hukumar EFCC tayi da kuma kwamitin wucin gadi da aka kafa wanda Aminu Waziri Tambuwal ya jagoranta, kan binciken yanda aka kashe kudi wajan gyaran wutar lantarki a zamaninshi sun wankeshi daga dikkan wani zargi.

Obsanjon ya kara da cewa ya kuma yi bayani dalla-dalla akan badakalar gyaran wutar lantarkin ta zamanin mulkinshi a cikin littafin da ya rubuta na My Watch, dan haka ya bukaci Buharin da 'yan koranshi da suje su karanta fannoni 41, 42, 43 da 47 na littafin nashi.

Ya kara da cewa, idan kuma Buharin bazai iya karantawa ba to yasa masu taimakamishi su karanta mai su kuma fassaramai a yaren da yafi fahimta.

Ya kara da cewa, mutane su fahimci cewa dala biliyan 16 da ake maganar kashewa a zamanin mulkinshi ba fa shine da kanshi yace ya kasheta ba, a'a zargi ne aka yi kuma tuni ya wanke kanshi, kamar yanda The Nation ta ruwaito.

No comments:

Post a Comment