Tuesday, 12 February 2019

Kungiyar Izala Bangaren Jos Ta Cimma Matsayar Sake Zaben Buhari>>Sheik Sani Yahaya Jingir

Kungiyar Jama'atu Izalatil bid'ah Wa'ikamatis Sunnah Assasawar Marigayi Ash Sheikh Isma'ila Idris bn Zakariyya Jos Wanda Ahalin Yanzu Ash Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir Yake Jagoranta, Ta yi Zama Tare da dukkan Shugabanninta Mataki na kasa.


Cikin wadanda aka yi zaman da su sun hada da Shugaban Majalisar Malamai na kasa Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir, shugaban kungiya na kasa (Admin), Sheikh Nasir Abdulmuhyi, Shugaban Rundunar Agaji Na kasa Sheikh Isah Waziri Muhammad Gombe, Shugabannin Malamai na jihohi 36 da Shugabannin Admin na jihohi Da na Agaji, a ranar Asabar 9/2/2019 Kungiyar ta yi zama na musamman a Babban ofishinta na kasa dake Jos babban birnin jihar Filato, inda Kungiyar Ta yi Matsaya na Sake Zaban Shugaban Kasa Muhammadu Buhari A Karo Na Biyu domin Ayyuka na Alkairi da Faro Ya karasa Cikin Aminci.

Wannan Matsaya Kenan Na Kungiyar Izala Mai hedkwata a Jos.


No comments:

Post a Comment