Wednesday, 6 February 2019

Kwamishinan Labarai na Tambuwal ya canja sheka daga PDP zuwa APC

Kwamishinan labarai na gwamnan jihar Sakkwato, Bello Muhammad Goronyo ya canja sheka daga jam'iyyar PDP zuwa jam'iyyar APC, dalilin haka kuwa gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya tumbukeshi daga mukaminshi.

Gwamnan ya bayyana cewa ya cire Bello ne saboda zagon kasa da yakewa tafiyarshi sannan ya baiwa babban sakataren ma'aikatar umarnin ci gaba da gudanar da ma'aikatar nan take, kamar yanda Punch ta ruwaito.

No comments:

Post a Comment