Saturday, 16 February 2019

Kwamitin yakin neman zaben Buhari sun dorawa PDP laifin dage zabe

Bayan da hukumar zabe ta sanar da dage zaben shugaban kasa dana majalisun tarayya wanda a da aka tsara yinshi yau, Asabar 16 ga watan Fabrairu zuwa Asabar ta sama, 23 ga wata 'yan Najeriya da dama sun mayar da martani akai, bangaren kwamitin yakin neman zaben shugaba Buhari ma ba'a barshi a bayaba inda su sukace laifin jam'iyyar PDP ne dage zaben.Me magana da yawun kwamitin yakin neman zaben na Buhari, Festus Keyamo ya bayyana rashin jin dadinsu da dage zaben bayan da shugaba Buhari ya baiwa Hukumar zaben dukan hadin kai ta hanyar samar musu da duk abinda suke bukata dan gudanar da zabe cikin nasara, injishi.

Festus Keyamo yace, yana horon INEC da ta ci gaba da zama 'yar ba ruwanmu tsakanin harkar siyasar jam'iyyu dan kuwa suna sane da rade-radin da ke yawo cewa dage zaben be rasa nasaba da rashin shirin jam'iyyar adawa ta PDP.

Ya kara da cewa dukkan alamu da kuma masu hasashe daban-daban sun hangowa PDP din faduwa a zaben shiyasa suka bugaci dage zaben dan su samu su sarara su kuma yin kokarin fito da wata sabuwar hanyar da zasu jawowa Buhari matsala dan kada yaci zaben.

Yace a shekarar 2015 ma saida PDP ta yi haka da taga cewa ba zata ci zaben ba.

Yace kuma tuntuni sun hango wannan shiri na PDP kuma sun kwarmatashi, ya kara da cewa tun a safiyar jiya, Juma'ane wasu manyan magoya bayan PDP suka wallafa a shafukansu na sada zumunta cewa za'a dage zabe amma daga baya suka goge sakon suka kuma bayar da hakuri wanda hakan na nuna cewa suna da shirin tun tuni.

Festus Keyamo ya bukaci 'yan Najeriya da su baiwa INEC din cikakken goyon baya akan wannan dage zabe dan basu so su yanke tsammani akan INEC din yanzu lura da abinda hakan zai iya haifarwa.

No comments:

Post a Comment