Sunday, 10 February 2019

Kwana daya da komawar Adam A. Zango bayan Atiku shi kuma Momo ya yadda Atiku ya dawo bayan Buhari

Kwana daya da sanar da ficewarshi daga jam'iyyar APC, tauraron fina-finan Hausa kuma mawaki,Adam A. Zango inda ya bayyana cewa rashin daukarshi da muhimmanci ne yasa yayi watsi da jam'iyyar to a yanzu abokin aikinshi, Aminu Shariff, Momo wanda ada yake tare da Atikun shi kuma yayi canjin sheka ya dawo bayan Buhari.Momo da ya saka wannan hoton da yayi inkiyar 4+4 dake nuna goyon bayan shugaba Buhari a shafinshi na sada zumunta ya samu yabo da tarba daga masoya da abokan arziki.

No comments:

Post a Comment