Friday, 15 February 2019

Mafi yawan Alkawuran da Buhari yayi be cikasu ba dan haka a baiwa Atiku dama shima idan bai cika alkawuranshi nan da shekaru 4 ba sai a canjashi>>Sani Musa Danja

Tauraron fina-finan Hausa, Sani Musa Danja, Zaki wanda yana daya daga cikin na gaba-gaba a masana'antar Kannywood wajan tallata dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya bayyana cewa mafi yawan alkawuran da Buhari yayi be cika su ba.A cikin wani jerin jawabi da yayi a shafinshi na sada zumunta Sani Danja yace, ya kamata idan mutane sun ga abinda ba daidai ba a gwamnati su rika fitowa suna fada dan hakan shine soyayya kuma ta hakane gwamnatin zata san da kuskurenta ta gyara.

Yace a da Boko Haram kawai aka sani amma yanzu ga fulani makiyaya masu kai hari, ga satar mutane a Zamfara dadai sauransu.

Yace da ace yanda ake tururuwa wajan yakin neman zabe haka gwamnoni suke tururuwa a Zamfara saboda gano hanyar magance kisan da akewa mutane da ba haka ba.

Ya kara da cewa, mafi yawancin alkawuran da Buhari yayi be cika ba dan haka a zabi Atiku Abubakar shima nan da shekaru 4 idan aka ga be cika alkawuran da ya dauka ba sai a canjashi.

No comments:

Post a Comment