Monday, 18 February 2019

Maganar shirin canja shugaban INEC ba gaskiya bane>>Fadar shugaban kasa

Fadar shugaban kasa ta musanta rade-radin dake yawo cewa wai shugaban kasa, Muhammadu Buhari na da shirin canja shugaban hukukar zabe me zaman kanta, INEC, Farfesa Mahamood Yakubu daga mukaminshi.Me magana da yawun shugaban kasar, Malam Garba Shehune ya tabbatarwar da jaridar The Nation hakan inda yace masu waccan magana su je su duba kundin tsarin mulki su ga yanda ake sauke da kuma canja shugaban hukumar zabe, shugaban kasa na bukatar goyon baya me rinjaye sosai daga majalisar tarayya kamin ya iya sauke shugaban hukumar zaben.

Bayan dage zaben da INEC ta yi shugaban jam'iyyar APC, Uche Secondus ya zargi cewa shugaban kasa,Muhammadu Buhari na shirin canja shugaban na hukumar zabe ya saka wanda zai iya juyawa dan ya bashi damar ci gaba da darewa akan mulki.

No comments:

Post a Comment