Saturday, 16 February 2019

MALAMAI MAGOYA BAYAN GANDUJE DA KWANKWASO AN YI ABIN KUNYA

Misalin abinda yake faruwa tsakanin wasu malamai masoya Kwankwaso da Ganduje, an dai yi abin kunya, lamarin babu dadin ji, tun farko banso 'yan uwa matasa da dalibai su zafafa wajen cin mutuncin Kwankwaso don ya taba malamai ba, domin yafi masu masa raddi karfin hujja da sanin sirrin Malaman a matsayinsa na tsohon gwamna kuma shugaba


Daga karshen al'amari dai wasu manyan jibga-jibgan Malamai da duniya take jin muryansu dake mara wa Kwankwaso baya sunje har gidansa sun bashi hakuri, Malaman suka dinga yiwa juna tone tonen asiri, ba'a kan komai ba face rigima akan kudi da ci-da-addini kowa yana kare miyarsa, har wadanda suka yiwa Kwankwaso zazzafan raddi sai da abin ya basu mamaki.

Wannan abin tsoro ne, domin har sai mutum ya rasa wani Malami zai kama. Allah Ka jikan Malam Ja'afar da Albaniy Zaria, wadannan sune Malaman al'umma wadanda Allah kawai suka sa a gaba ba duniya ba, rayuwarsu abin kwatance ne

Malam Albaniy Zaria lokacin da yake raye ya taba fadin cewa bari na fada muku gaskiya; zaiyi wahala a sake samun Malami mai takawa da tsoron Allah a Nigeria kwatankwacin Marigayi Sheikh Abubakar Mahmud Gumi saboda yadda al'umma ta lalace Malamai irinsa basu dace da wannan zamanin ba

To kamar hakane tabbas su Sheikh Albaniy Zaria da Malam Ja'afar Kano  basu dace da wannan zamanin namu ba, Allah Yayi amfani dasu wajen isar da sakon addininSa, bai barsu sun jima a cikinmu ba duk da dunbin ilmi da suka tara, sai Allah Ya karbe abinSa, Ya musu kyauta da mafi alherin karshen sakamakon wato mutuwar shahada kamar yadda muke musu fata

Muna rokon Allah Ya jikansu da rahama.
Daga Datti Assalafiy


No comments:

Post a Comment