Monday, 11 February 2019

Manchester City ta wa Chelsea cin rabani da yaro 6-0

Manchester City ta sake dare kan teburin Premier, bayan da ta ragargaji Chelsea a wasan mako na 26 da suka fafata a Ettihad a ranar Lahadi.


City ta yi nasarar doke Chelsea da ci 6-0, kuma Sergio Aguero ne ya ci kwallo uku, sai Raheem Sterling da ya ci biyu sannan Ilkay Gundogan da ya zura daya a raga.

Kwallayen da Aguero ya ci uku rigis a karawar sun sa ya yi kankankan da Alan Shearer da ya yi bajintar hakan sau 11 a tarihin gasar Premier.

Da wannan sakamakon Manchester City ta koma ta daya da maki 65 a kan teburin Premier, inda Liverpool ta koma ta biyu duk da maki 65 da take da shi, sannan Tottenham ta uku da maki 60.

Chelsea kuwa ta koma ta shida da maki 50, Arsenal ta zama ta biyar kenan duk da maki 50 da take da shi, inda Manchester United ta koma ta hudu, bayan da ta yi nasarar doke Fulham 3-0 a ranar Asabar.

City ta taba doke Chelsea 6-2 a ranar Asabar 26 ga watan Nuwambar 1977 tun a wasan rukuni na farko kan a kai sauya wa Premier fasali.

Chelsea da Manchester City za su sake haduwa a wasan karshe a Caraboa Cup a ranar Lahadi 24 ga watan Fabrairu a Wembley.
BBChausa.


No comments:

Post a Comment