Sunday, 10 February 2019

Manchester United ta koma ta 4 a Firimiyar Ingila


Likkafar Manchester United na ci gaba da dagawa a gasar Premier ta Ingila, bayan da kungiyar ta lallasa takwararta Fulham da kwallaye 3-0.

Nasarar ta bai wa United damar komawa mataki na 4 a gasar ta Premier daga matsayi na 6 da ta ke kai a baya.

‘Yan wasan Manchester United Paul Pogba da Martial ne suka jefa kwallayen a ragar Fulham.

Karo na farko kenan da Manchester United ta samu nasara a jimillar wasanni 6 da ta fafata a gidan abokan karawarta, tun bayan irin bajintar da ta nuna a kakar wasa ta 2009 cikin watan Mayu.

Tun bayan karbar ragamar jagorancin United da Ole Gunnar Solskjaer ya yi daga hannun Jose Mourinho, kungiyar ta samu nasara a wasanni 10, daga cikin jimillar wasanni 11 da ta fafata.

Ranar Talata 12 ga watan Fabarairu, Manchester United za ta yi tattaki zuwa Faransa, domin fafata wasan zagayen farko tsakaninta da kungiyar PSG, a gasar zakaru nahiyar Turai.
RFIhausa.

No comments:

Post a Comment