Wednesday, 13 February 2019

Manchester United ta yi rashin nasara mafi muni a hannun PSG

Kungiyar Manchester United ta yi rashin nasara mafi muni a tarihin buga gasar cin kofin zakarun turai a hannun PSG da ci 2-0, a tarihin Man U ba'a taba yin nasara akanta ba da kwallaye fiye da daya ba a gida.Duk da babu taurarin 'yan kwallonta guda biyu, Edinson Cavani da Neymar amma PSG ta yi nasara akan Man U da kwallaye biyun da Presnel Kimpembe da Kylian Mbappe suka ci mata.

Pogba ya samu jan kati ana kusa da kammala wasan wanda hakan ke nufin bazai buga wasa na gaba da Man U zata je gidan PSG ba, wannan ne karin farko da me horas da Man U, Ole Gunnar Solskjaer yayi rashin nasara a wasanni 12 da ya buga.

Kuma PSG ta kafa tarihin zama kungiyar kwallon kafar kasar Faransa ta farko da ta yi nasara akan Man U a gida, Old Trafford.

Masu sharhi dai na ganin da wuya Man U ta tsallake matakin 'yan aji 16 na gasar musamman ganin cewa wasanta na gaba zata bugashi babu Pogba.

No comments:

Post a Comment