Saturday, 16 February 2019

Maryam Gidado ta ji kiran Adam A. Zango ta cire hotonta da ya jawo cece-kuce

Bayan da tauraruwar fina-finan Hausa, Maryam Gidado ta saka wani hoton bidiyo a dandalinta na sada zumunta da ya dauki hankula sosai akai ta cece-kuce akai wanda har Adam A. Zango ya saka baki a ciki inda ya bukace ta da ta cire hoton, Maryam din dai ta ji kiran na Adamu ta cire wancan hoto.Wannan dai na nuna cewa Maryam din na jin maganar Adamu.

Ko da a lokacin da Adam A. Zangon ya koma jam'iyyar PDP daga APC, Maryam na daya daga cikin wanda suka fito suka kare shi daga masu sukarshi har shima ya bayyana cewa yasan ko wuta ya shiga Maryam din zata bishi.

No comments:

Post a Comment