Wednesday, 13 February 2019

Mbappe ya kamo Ronaldo a yawan kwallaye a gasar cin kofin zakarun turai

Tauraron dan kwallon kafar kasar Faransa me bugawa kungiyar PSG wasa, Kylian Mbappe ya kamo tsohon dan kwallon Brazil da Real Madrid, Ronaldo a yawan kwallaye a gasar cin kofin zakarun turai.Dan shekaru 20, Mbappe yaci kwallaye 14 kenan a gasar a wasanni 24 da ya buga yayin da shi kuma Ronaldo ya ci kwallayen 14 a wasanni 40 da ya buga a zamaninshi.

Irin salon da Mbappe ke buga wasa ana ganin zai iya bin sahun Cristiano Ronaldo da Messi a yayinda a yanzu Robaldonne keda mafi yawan kwallaye a gasar ta cin kofin turai da kwallaye 121 a wasanni 158 da ya buga yayinda Messi ke take mai baya da kwallaye 106 a wasanni 129 da ya buga.


No comments:

Post a Comment