Tuesday, 19 February 2019

Me doka ta ce kan barawon akwatin zabe?

Tun bayan da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana cewa duk wanda ya saci akwatin zabe ya yi a bakin ransa, 'yan kasar suke ta cece-kuce a kan wannan kalamai na sa.


A wannan dalili ne ya sa BBC ta tuntubi wani lauya a Najeriya watau Dakta Aminu Gamawa, a kan ko me doka ta ce a kan wanda ya saci akwati.

Dakta Aminu dai ya bayyana cewa dokar kasar ta hana sace akwatin zabe kuma duk wanda aka samu da laifin yin hakan, za a iya yanke masa hukuncin zaman gidan yari na kusan shekaru biyu.


Ya bayyana cewa idan aka kama barawon akwatin zabe, jami'an tsaro su kamashi su bincike shi sa'annan a gurfanar dashi gaban kotu.

Lauyan ya kuma ce bai kamata a ce idan an kama barawon akwatin ba an dauki doka a hannu, ya ce kotu ce kadai ke da hurumin hukunta shi.

An dade ana fama da batun satar akwatin zabe a Najeriya a lokacin zabe inda ake samun 'yan barandan siyasa suna irin wannan aika-aika.

Tuni dai wasu manya a jam`iyyar APC suka ce shugaban kasar gargadi ne kawai yake yi.

inda suka ce jama'a da dama sun jahilci kalaman na shugaban kasa.

Babbar jam`iyyar hamayyar kasar dai, wato PDP ta yi zargin cewa shugaban kasar na so ne ya yi amfani da jami`an tsaro wajen dakile `yan adawa.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment