Friday, 8 February 2019

Mutumin da aka ruwaito cewa ya saki matarshi saboda tace sai ta zabi Buhari yace be saketa: Abokanshine kawai suka tsara karya

Labarinnan na mutumin da ya saki matarshi saboda ta dage sai ta zabi shugaban kasa, Muhammadu Buhari kamar yanda BBChausa ta ruwaito kwanannan ba gaskiya bane bisa binciken da jaridar Daily Trust ta yi.Wakilin Daily Trust ya garzaya kauyen Unguwan Gero inda Abdullahi Yada’u da matarshi, Fatima ke zaune kuma dukansu sun musanta wancan labari, inda suka tabbatarwa da jaridar cewa basu yi fada a tsakaninsu ba.

Wakilin Daily Trust yace mutanen da suka yi magana da BBC ba ma'auratan bane sun ari bakinsune suka ci musu Albasa, ya kara da cewa a lokacin da ya isa kauyen ya tarar da Fatima tana wa daya daga cikin 'ya'yansu wanka.

Sannan ta gayamai cewa, shekararsu 7 kenan da mijinta kuma ba ta ji dadin wannan labari da aka watsa ba dan an yine saboda a kawo musu matsala a aurensu, ta kara da cewa mutane 'yan uwa da abokan arziki sun rika tururuwa gidan nasu suna musu jaje.

Ta kara da cewa basu yi gardamar siyasa ita da mijinta ba dan dukansu masoya Shugaban kasa, Muhammadu Buharine.

Shima mijin, Abdullahi Yada’u yace hirace kawai suke a majalisar su da suke zaune sai aka tattauna siyasa shine wani yace a saka labarin a yanar gizo wasu kuma suka ce zai fi kyau a saka a gidan rediyo kamar BBC, yace sun sameshi amma yace shi da wasa yake sannan ya bar gurin.

Ya kara da cewa, abokanshine suka tafi a bayan idonshi suka kira BBC aka yi hira dasu, yace har saida 'yansanda suka gayyaceshi ya bayar da rahoton cewa ba shine yayi wannan abu ba sannan abokan nashi yanzu sun tsere.

Yace abin ya firgitashi sosai dan sai da yayi tunanin tserewa.

No comments:

Post a Comment