Monday, 18 February 2019

Na janye tsinuwar da nawa wanda basa son Buhari amma har yanzu ina kira da a zabeshi>>Sheikh Gero Argungun

Shehin malamin addinin Islama, Sheikh Abubakar Gero Argungun ya fito ya bayar da hakuri akan la'anar da yayiwa wanda basa goyon bayan shugaban kasa, Muhammadu Buhari.A cikin wani faifan bidiyo da ya saki, Malamin ya bayyana cewa bidiyonshi da ake yadawa a shafukan sada zumunta inda aka nunashi yana cewa Allah ya kwashewa duk wanda baison Buhari Albarka da gaskene, hakan ya faru amma tun lokacin mulkin Jonathan ne a lokacin da ake fama da hare-hare ta yanda yanayin da ake ciki ke sa mutum yayi irin wadancan kalamai.

Malamin ya kara da cewa kuma bama a Najeriya yayi wancan wa'azi ba amma dai duk da haka maganar tsinuwa da yayi ya yadda cewa akwai kuskure a ciki kuma ya janye.

Saidai ya kara da cewa har yanzu yana nan kan bakanshi na jama'a su fito su sake zaben shugaban kasa, Muhammadu Buhari ranar Asabar.

No comments:

Post a Comment