Friday, 8 February 2019

Nura M. Inuwa ya bar tafiyar Atiku: Yace ba ruwanshi da kowane dan siyasa dan ya duba bega Mafita ba

Tauraron mawakin Hausa, Nura M. Inuwa wanda ada ake mai kallon dan PDP wanda har yawa dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar waka yanzu ya fito ya nesanta kanshi da duk wani dan siyasa inda yace bazai kara saka hoton wani dan siyasa a shafinshi ba idan kuma akwai wanda ya biyashi ya mai yalla to yasa a kamashi.Nura yayi wannan rubutune a shafinshi na Instagram inda ya bayyana takaici akan salon siyasar kasarnan wanda yace tun yana yaro ya taso ya ganta kuma yana cikin wahala sannan be ga alamar canji ba, yayi iya bincikenshi dan haka zai ja da baya.

Ga abinda ya rubuta kamar haka:

'Abun tunani da tambaya shine kowa ya fito so yake a zabeshi, shin bbu wani wanda ya fahimci siyasa da zai tsayawa talaka? naso ace akwai wani dan gwagwar maya daya da zai tsaya ya jajirce ya shige gaba wajan wayar da kan Al'umma su san matsayin masu neman matsayin a gurinsu,inda hali ma ya zama silar da zai hana talaka fita filin zabe tunda tun kafin nazo duniya aketa fama a haka kakanin mu sun wahala iyayen mu sun wahala muma muna wahala kuma banga alamar da zata hana 'ya'yanmu shan wannan wahalar a hannun mutanan nan ba,sai ikon ALLAH,duk lokacin dana tuna haka takaici yana isata nayi kokari ta hanyar da ALLAH ya nufe ni nayi waka mai suna na gane duniya,nayi samari, kusa kusa akwai waka da nake cewa 'yanci ya siyo raini a cikinta duk dan na haskawa mutane wasu abubuwa, amma na fahimci sakona baya zuwa inda nakeso ta bangaren nan zan kama baki na,bbu wani abu da nake fata na samu al'umma su shiga damuwa a duniya,kuma bani da mai gida a siyasa dana taba kaiwa matsalata koda ta kwandala ce duk abunda ka ganni dashi daga ALLAH ne sai kuma masoya da baza su gogu a zuciyata ba,nayi alkawarin har siyasa ta huce bazan saka gunkin ko wanne dan takara a page dina ba, idan akwai wanda ya bani kudi domin nayi tallansa banyi ba ya kama ni,bana bukatar kudin sawa a aljihu makomar al'umma nake duba, amma nazarina ya kare ban hango mafita ba.Don haka zan ja da baya na ci gaba da yin Addu'a ALLAH ya kawo mana mafita...'

No comments:

Post a Comment